in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping da Barack Obama sun gana da manema labaru tare
2013-06-08 18:51:09 cri

A ranar 7 ga wata, agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama sun yi shawarwari na zagaye na farko. Bayan ganawar, su biyu sun gana da manema labaru tare a Annenberg Retreat na Sunnylands dake jihar California ta kasar Amurka.

A yayin taron manema labaru, Xi Jinping ya ce, ya yi ganawa ta zagaye na farko da shugaba Barack Obama dazu, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan manufofin cikin gida da na waje na kasashensu, batun kafa sabuwar huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, da sauran batutuwan da suke jawo hankulansu tare. Su biyun sun cimma matsaya daya kan wadannan batutuwa.

Sannan Xi Jinping ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan matsayinta na neman ci gaba cikin lumana, karfafa yin gyare-gyare daga dukkan fannoni, kara bude kofarta ga kasashen waje, kuma za ta yi kokarin cimma kasaitaccen burin al'ummar Sinawa, ta yadda za a iya kara tabbatar da zaman lafiya da ciyar da duk duniya gaba.

Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, mista Obama da shi dukkansu biyu suna ganin cewa, yayin da ake raya tattalin arzikin duniya baki daya cikin sauri, kuma ana bukatar kasa da kasa da su taimakawa juna, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su lalubo wata sabuwar hanya, a kokarin magance ta da rikici a tsakanin manyan kasashe. Kana kasashen 2 sun amince da yin kokari tare wajen kafa hulda ta sabon salo a tsakaninsu, za su girmama juna, da yin hadin gwiwa domin samun moriyar juna, a kokarin kawo alheri ga jama'arsu da ma ta duk duniya baki daya. Sa'an nan kuma kasashen duniya na sa ran ganin huldar da ke tsakanin Sin da Amurka ta yi ta kyautata da bunkasa. Kyakkyawar hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Amurka za ta kara azama kan tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a duk fadin duniya.

A nasa bangaren, shugaba Obama ya ce, Amurka da Sin na bukatar kara wa juna fahimta dangane da manyan tsare-tsare. Za su iya samu ci gaba a fannin inganta huldar da ke tsakanin sojojin kasashen 2, wanda kuma shi abun shaida ne na kara kuzari kan kafa hulda ta sabon salo a tsakanin Amurka da Sin. Wajibi ne kasashen 2 su dauki matakai wajen kafa tsari kan yin tattaunawa a tsakaninsu a lokaci-lokaci. Har wa yau kuma, bunkasuwar kasar Sin cikin lumana na dacewa da moriyar kasarsa ta Amurka sosai. Idan kasar Sin ta samu nasara, to, za a sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya, haka kuma za a mayar da kasar Sin a matsayin abokiyar Amurka, wadda ta yi zaman daidai wa daida da Amurka, ta yadda kasashen 2 za su iya tinkarar dimbin kalubalolin kasa da kasa cikin hadin gwiwa. Hadin gwiwar da ke tsakanin Amurka da Sin za ta ba su kyakkyawar damar tabbatar da manufofinsu ta fuskar tsaro da samun wadata. (Sanusi Chen, Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China