Daga ranar 31 ga watan Mayu zuwa ranar 6 ga watan Yuni ne dai shugaba Xi Jinping, ya gudanar da ziyarar aiki a kasashen Trinidad and Tobago, da Costa Rica, da Mexico. Daga bisani kuma ya gana da shugaba Obama na kasar Amurka, daga ranar 7 zuwa ta 8 ga wata, a jihar California dake kasar.
Ganawar da shugaba Xi ya yi tare da takwaransa na kasar Amurka Obama, ta kasance karon farko da shugabannin kasashen 2, suka yi musayar ra'ayi ido da ido, tun bayan da Xi ya hau karagar mulki, kuma Obama ya sake zama shugaban kasar Amurka. Kana hakan ya kasance karo na 2 da shugabannin 2 suka gana da juna a shekaru 2 da suka wuce.
Yayin ganawar tasu, shugabannin 2 sun tattauna kan yanayin da kasashensu ke ciki a fannin tattalin arziki, da huldar dake tsakanin bangarorin 2 a wannan fanni, da matakan da za a dauka don raya huldar dake tsakaninsu, gami da sauran batutuwan dake janyo hankalinsu, inda suka cimma matsaya guda.
A cewar Xi Jinping, ganawar ta nuna alamar cewa kasashen 2 za su kara yin musayar ra'ayi, don inganta amincewa juna, da kyautata huldar dake tsakaninsu, don tabbatar da zaman lafiya da walwala a yankin Asiya da Pasific, gami da duniya baki daya. (Bello Wang)