in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping na Sin da Barack Obama na Amurka sun yi ganawar farko
2013-06-08 09:56:36 cri

Shugaba Xi Jingping na kasar Sin, da takwaransa Barack Obama na kasar Amurka sun yi ganawar farko a ranar Juma'a 7 ga wata can a Rancho Mirage, dake jihar Californian kasar ta Amurka, a wata ganawa irinta ta farko da ake fatan za ta ba su damar tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kasashen nasu.

Shugaban kasar ta Amurka ya tarbi shugaba Xi, tare da yi masa maraba a wani babban gidan shakatawar shugaban kasa dake jihar ta California, inda kuma suka yi wa juna marhaban da lale. Bayan wannan ganawa ta farko, shugabannin biyu za su tattauna da juna da yammaci, sa'an nan za su sake gudanar da wata tattaunawar da safiyar Asabar 8 ga wata.

Wannan tattaunawar ido-da-ido da jagororin biyu za su yi, ita ce irinta ta farko, tun bayan da kasashen Sin da Amurka suka kammala babban zabe, da ya samar da sabbin jagororin kasashen biyu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China