in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi ganawa da takwaransa na kasar Amurka karo na biyu
2013-06-09 09:39:42 cri

A ranar 8 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi ganawa karo na biyu da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama a wurin hutawa na Annenberg dake jihar California ta Amurka, inda shugabannin kasashen biyu suka tattauna halin tattalin arziki dake cikin kasashensu da manufofin tattalin arziki da suke bi, kana sun yi musayar ra'ayi game da karfafa dangantakar bangarorin biyu a tsakaninsu.


Mr. Xi ya yi nuni da cewa, dangantakar tattalin arziki ta zama babban tushe wajen raya dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka. Ya ba da shawara ga bangarorin biyu da su inganta hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin saka jari na bangarorin biyu, raya makamashi, da manyan ababen more rayuwa, da inganta hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomi na kasashen biyu, gami da manyan tsare-tsare da sauransu.
Xi Jinping ya bayyana cewa, ganawar da aka yi ta wannan karo ta kasance na tuntubar juna da mu'amala karo na farko bayan da aka yi babban zabe a kasashen biyu, kuma abin tarihi ne na mu'amalar manyan jami'an kasashen biyu. Haka kuma, abin da ya nuna wa kasashen duniya da jama'ar kasashen biyu cewa, sun dukufa ka'in da na'in wajen inganta mu'amala, da amincewar juna bisa manyan tsare-tsare, don kafa sabon nau'in dangantakar tsakanin manyan kasashen biyu, tare da sa kaimi ga samar da zaman lafiya da karko da wadata a yankunan Asiya da Fasifc da kasashen duniya baki daya, ganawar ta samu sakamako mai gamsarwa.


A nasa bangare kuma, Obama ya ce, dangantakar tattalin arziki da ke tsakanin kasashen Amurka da Sin tana shafar samun karko da wadata a kasashen biyu, kuma ya yi babban tasiri game da tattalin arziki na duniya. Amurka tana sa kaimi ga masana'antun Sin da su saka jari a kasar Amurka, da daukar matakai wajen kawo sassauci wajen fitar da kayayyakin fasahohin zamani zuwa kasar Sin, kuma yana fatan inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya da makamashi tsakanin kasarsa da Sin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China