in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan adawan Syria suna nazarin matsayarsu game da taron Geneva a Istanbul
2013-05-24 10:50:48 cri

A ranar Alhamis, babbar kungiyar adawa ta kasar Syria ta yi zaman tattaunawa a Istanbul na kasar Turkiya dangane da matsayarta game da taron kasa da kasa da za'a yi a Geneva.

Za'a yi kwanaki uku ana sabon zagayen tattauanawan, inda a wannan lokaci, kungiyar National Coalition za ta zabi shugabanta wanda zai maye gurbin Chief Moaz Al-khatib wanda ya yi murabus.

Wasu manyan jami'an kungiyar tun da farko sun ce, 'yan adawar na bukatar samun tabbaci dangane da murabus din shugaba Bashar al-Assad da kuma samun karin makamai wa mayakan kungiyar a matsayin batutuwa da za'a shigar cikin kowace irin yarjejeniyar mika mulki.

'Yan adawar har ila yau za su tattauna kan fadada hadin gwiwarsu da sabbin mambobi da kuma makomar gwamnatin rikon kwaryar.

A ranar Laraba ne kungiyar abokan kasar Syria ta yi wata ganawa a Jordan, inda ta yi kira da a kafa gwamnatin riko a matsayin wata hanyar kawo karshen zub da jinni da kuma shirin gudanar da taron kasa da kasa a Geneva cikin watan Yuni.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China