Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon a jiya Litinin ya fara ziyarar aiki na yini biyu a kasar Mozambique, wanda a lokacin wannan ziyara, zai yi musayar ra'ayi da jami'an kasar a kan shirin muradun karni na MDD da kuma halin da ake ciki a DRC jamhuriyar demokradiya ta Congo.
Mr. Ban ya riga ya gana da madam Veronica Macamo, shugaban majalissar dattaijai ta kasar a jiya Litinin daga isarsa. Kuma ana sa ran zai halarci tattaunawa a kan taken 'A nan gaba muna son shirin muradun karni bayan shekara ta 2015 da abin da zai biyo baya a 2025', sannan kuma ya gana da shugaban kasar Armando Guebuza a yau Talata, kamar yadda jadawalin ziyarar ta nuna.
Shugaban kasar Mozambique a yanzu haka shi ke rike da shugabancin kungiyar cigaban tattalin arzikin kasashen 14 na kudancin Afrika, wanda DRC take 'yar kungiyar.
Ganawar da shugaba Guebuza ta taka muhimmiyar rawa wajen rattaba hannu a kan yarjejeniyar ganin an samu zaman lafiya da aka yi a watan Fabrairu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya bayyana.
Ita dai kasar Mozimbique ita ce zangon farko na ziyarar Mr. Ban a nahiyar Afrika. Zai ziyarci jamhuriyar demokradiya ta Kongo a ranar Laraba 22 ga wata zuwa Alhamis 23, sannan zai isa Ruwanda daga 23 ga wata zuwa 24, sai zangon shi na karshe a wannan ziyarar aiki da zai yi a kasar Uganda a ranar 24 ga wata, a sanarwa MDD.(Fatimah)