in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batun warware rikicin Somaliya na cikin muhimman batutuwa, in ji MDD
2013-06-05 10:50:22 cri

Yayin da kwamitin tsaron MDD ke ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron birinin Geneva don gane da kasar Sham, a hannu guda, rikicin kasar Somaliya na ci gaba da daukar hankulan masu ruwa da tsaki. wannan kalamai sun fito ne daga bakin jagoran kwamitin tsaron MDD na wannan wata, kuma jakadan Birtaniya a majalissar Mark Lyall Grant.

Grant wanda ya zanta da manema labarai a ranar Talata 4 ga watan nan, ya ce, kare martabar bil'adama, da hana cin zarafin al'umma, da kare albarkatun kasar ta Somaliya, na cikin muhimman lamurran da za a baiwa muhimmanci a ajandar kwamitin tsaron na wannan wata.

A cewarsa, baya ga batun kasar Sham dake kan gaba, batun dorawa inda aka tsaya, don gane da taron birnin Landan da ya gabata kan kasar Somaliya ne ke biye, cikin muhimman babutuwan da kwamitin tsaron mai kunshe da kasashe 15 suka tattauna a taronsu na sirri.

Cikin muhimman shirye-shiryen da ake gudanarwa, a cewar jagoran kwamitin, akwai taron tattaunawa da ake fatan wakilin kasar Birtaniya mai lura da Afrika Mark Simmonds zai halarta a ranar Alhamis, yayin da mataimakin babban sakataren MDD Jan Eliasson zai gabatar da jawabi gaban mambobin kwamitin.

Sai kuma wani taron mahawara don gane da batun kare barkewar rikici, da kiyaye albarkatun kasa da za a gudanar a ranar 19 ga watan Yunin nan, wanda zai mai da hankali ga nazarin yadda kyakkyawan yanayin masana'antun hakar ma'adanai ka iya kandagarki ga barkewar rigingimu, yaki da cin hanci da rashawa, ya kuma tallafa wajen kare hakkokin bil'adama, tare da habaka ci gaban rayuwar al'umma.

Har ila yau, za a gudanar da taron kare al'ummar da rikice ke shafar yankunansu daga cin zarafi a ranar 24 ga wata, taron da ake fatan sakataren wajen kasar Birtaniya William Hague zai jagoranta. Ana kuma sa ran babban magatakardar MDD, da kuma wakiliyarsa ta musamman don gane da dakile ta'adar cin zarafin bil'adama Zainab Hawa Bangura za su halarci wannan taro. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China