Sabon wakilin musammun na sakatare janar na MDD, mista Nicolas Kay ya isa Somaliya tun ranar Litinin domin kama ayyukansa na shugaban sabuwar tawagar siyasa ta MDD a wannan kasa, da na tawagar ba da tallafi ta MDD a kasar Somaliya (MANUSOM).
'Kasar Somaliya na alfahari da gargajiyarta, al'adunta da abubuwan tushenta. Zan yi duk wani kokari na kawo taimakona ga gwamnati da al'umma domin samun zaman lafiya, tsaro da wadata a kasar Somaliya.' in ji mista Kay tun daga birnin Mogadishu.
Jami'in na MDD ya kuma mika godiyarsa ga tsohon wakilin musammun kuma shugaban cibiyar MDD a kasar Somaliya, Augustine Mahiga, tare da bayyana cewa, wani sabon babi ne MDD ta bude a wannan kasa.
'Al'ummar Somaliya ta bayyana fatanta kan wannan sabuwar dangantaka da MDD da za ta cimma bukatun jama'a. Ayyukanmu za su rataya ga raya dangantaka mai karfi tare da kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU da sauran masu fada a ji. Gamayyar kasa da kasa ta sake jaddada niyyarta kan kasar Somaliya ta hanyar taimakawa tawagar MANUSOM.' in ji mista Kay.
Kwamitin tsaro na MDD ya amince wannan kuduri a farkon watan Mayu, kuma bisa yawan rinjaye na kasashe mambobi 15 na kwamitin, tawagar MANUSOM na da wa'adin aiki bisa karon farko na watanni 12 da zai fara wannan rana. Aikin tawagar MANUSOM shi ne taimakawa hukumomin kasar Somaliya wajen kokarin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan 'yan kasa, haka kuma da taimakawa gwamnatin kasar kulawa da taimakon da kasashe da kungiyoyi suke baiwa kasar, ta yadda za'a karfafa aikin samar da kasa mai 'yanci, da sa ido da rigakafin tashe-tashen hankalin dake nasaba da 'yancin 'dan adam a cikin wannan kasa. (Maman Ada)