A jiya Alhamis 6 ga wata, kwamitin tsaro na MDD ya yi kira ga kasashen duniya da su goyi bayan kasar Somaliya a kokarin da take yi na samun zaman lafiya mai dorewa, yana mai yaba ma ayyukan da kasar ta yi cikin wannan lokaci na ganin ta cimma hakan.
A cikin wata sanarwa, an ce, kwamitin a lokacin wani zaman taro na musamman da ya yi a kan kasar ta Somaliya karkashin jagorancin Mark Simmonds, 'dan majalissa karkashin ofishin harkokin waje da kasashen renon Ingila na kasar Birtaniya, wanda shi ke rike da shugabancin kwamitin na wannan watan, ya yi nuni da muhimmancin samar da goyon baya daga kasashen duniya ga Somaliya domin ta samu ta kafa ingantacciyar gwamnati mai kunshe dam asana da za su ba da cikakken kokarinsu wajen kafa doka da za ta kula da tsarin shari'a, hakkin bil adama da kuma doka da oda.
Kwamitin tsaron na MDD har ila yau ya bukaci kasashen duniya da su samar da tsari mai nagarta da zai ba da taimako wajen samar da kayayyakin agaji da dimbim al'ummar kasar da fadace-fadace ya daidaita.
Kwamitin ta kuma jaddada muhimmancin dake akwai ga hukumar ba da agaji ta majalissar dake kasar Somaliya wadda ta fara aiki a ranar Litinin din nan da ta ba da goyon baya ga shirin samar da zaman lafiya da tsaro na kasar Somaliyan. (Fatimah)