Babban magatakadar MDD Ban Ki-Moon, ya bayyana bukatar gaggauta warware rikicin kasar Somaliya, domin kare Kenya daga fadawa halin tsaka mai wuya. Ban Ki-Moon ya gabatar da wannan bukata ne yayin ganawarsa da mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto a kasar Japan, yana mai cewa, MDD na sane da irin kalubalen dake addabar kasar ta Kenya, don gane da burin ganin an shawo kan rigingimun dake addabar makwafciyarta wato Somaliya.
Babban magatakadar MDD ya kara da cewa, ya yi matukar takaicin ganin halin da 'yan gudun hijira ke ciki a sansanin Dadaab, yayin da ya ziyarci sansanin a shekarar 2012. Daga nan sai Ban ya ayyana bukatar dake akwai ga hukumomin kasa da kasa, da su tallafawa shirin sake wa kimanin 'yan gudun hijira 600,000 dake zaune a sansanonin arewacin kasar ta Kenya matsuguni.
A yanzu haka dai kasar ta Kenya ce ke baiwa dubban 'yan gudun hijira daga Somaliyan matsuguni, ko da yake dai Kenyan na ganin maida 'yan gudun hijirar zuwa kasashensu, zai taimaka matuka wajen kare kanta daga matsaloli masu alaka da tsaro. Sai dai sabanin wannan ra'ayi, hukumar MDD mai lura da harkokin 'yan gudun hijira, da ma wasu kungiyoyin ayyukan ji kai, na ganin mayar da 'yan gudun hijirar kasashensu a halin da ake ciki na iya jefa rayuwarsu cikin hadari
A nasa jawabi, Mr. Ruto cewa ya yi, warware matsalar 'yan gudun hijira, batu ne dake da matukar muhimmanci. Don gane da hakan ne ma ya ce, Kenya na fatan samun dukkanin goyon baya daga MDD.(Saminu)