in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sauke ministan tsaron kasar Libya daga mukaminsa
2013-06-28 10:30:46 cri

Firaministan kasar Libya Ali Zeidan ya fada a ranar Alhamis cewa, an sauke ministan tsaron kasar daga mukaminsa, sakamakon fadan da aka gwabza tsakanin 'yan tawayen da ke dauke da makamai wadanda ba su ga majici da juna a Tripoli, babban birnin kasar.

Firaministan ya ce, nan ba da dadewa ba za a nada sabon babban hafsan sojan kasa, bayan da Yussef al-Mangoush ya ajiye mukaminsa a wannan watan, sakamakon munanan hare-haren da aka kai a birnin Benghazi da ke gabashin kasar.

An ji karar abubuwan fashewa da harbe-harben bindiga ranar Laraba da dare a Tripoli, rana ta biyu na tashin hankalin da ya barke a birnin, inda mutane 10 suka mutu, kana sama da 100 suka jikkata, abin da ke nuna tsananin gabar da ke tsakanin kungiyoyin da ke dauke da muggan makamai da suka mamaye kasar tun lokacin da aka hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China