in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron Libya ya janye takardar barin aikinsa
2013-05-08 09:56:12 cri

Ministan tsaron kasar Libya, Mohammed al-Bargathi a jiya Talata ya janye takardar barin aikin da ya gabatar sa'o'i kadan da mika ta ga firaminista Ali Zaidan, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar ta sanar.

Wannan sauyin ra'ayin ya biyo bayan bukatar da firaministan ya nuna ma ministan tsaron da ya cigaba da aikinsa, ganin yadda al'amuran tsaro suka tabarbare a kasar.

A lokacin wani taron manema labarai tun da farko a jiya Talatan, ministan tsaron kasar Al-Bargathi ya sanar da cewa, ya mika takardar ajiye aikinsa saboda nuna rashin jin dadi a kan kawanya da wassu 'yan bindiga suka yi ma wassu ma'aikatun gwamnati na tsawon fiye da mako daya.

A wani labari kuma wani babban jami'in sojin kasar ya sheda ma kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa, babban hafsan sojin kasar Yousef Al-Mangoush shi ma ya mika takardar ajiye aikinsa a jiya Talatan, sai dai kuma wani ma'aikacin a karkashin babban hafsan ya musanta hakan a taron manema labarai.

Kakakin kungiyar al'ummar kasar Libya GNC ya sheda ma Xinhua cewar, kwamitin dake kula da rundunar sojin kasar ta jefa kuri'ar, inda suka amince da ya ci gaba da rikon mukamin, har nan da wata daya mai zuwa, wanda a cikin wannan lokacin za su duba abin da za'a iya yi, bayan hakan kuma in ba su cimma wani matsayi ba, to dole ya cigaba da rikon mukamin.

A makon da ya wuce ne, wassu gungun 'yan bindiga suka mamaye ma'aikatar shari'ar kasar da kuma ma'aikatar harkokin waje, suna bukatar amincewar a kebe harkokin siyasa daban da na doka, haka kuma suka bukaci da a dakatar da duk wadanda suka yi aiki a karkashin tsohon shugaban kasar Muammar al-Gaddafi daga rikon mukaman gwamnati.

Wannan kawanya dai ya dauki tsawon fiye da mako daya, duk da amincewar da aka yi masu cewar, an dakatar da duk wadanda suka taba aiki da tsohon shugaban kasar daga rike manyan mukamai a kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China