A ranar Laraba ne wasu fadace-fadace suka barke a Tripoli, babban birnin kasar Libya, tsakanin wasu kungiyoyi biyu da ke dauke da makamai, yayin da kuma wani mummunan tashin hankali ya yadu zuwa Benghazi da ke gabashin kasar.
Fadan, a cewar sojojin yankin, ya barke ne bayan wasu gungun masu dauke da makamai daga birnin Zintan da ke yammaci wadanda suka yaki magoya bayan tsohon shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi a yakin basasar shekarar 2011, suka yi kokarin sako 'yan uwansu da tsoffin 'yan tawayen gundumar Abu Salim da ke Tripoli suka kama ranar Talata.
A halin da ake ciki kuma, wata sanarwa a hukumance ta bayyana cewa, adadin wadanda suka jikkata ya karu, inda mutane 5 suka mutu, kana 22 suka raunata, bayan harin na ranar Talata da 'yan bindigar Zintan din suka kai kan masu gadin cibiyar na'urorin man fetur din Libya da ke Tripoli wanda a farko mutum guda ya mutu yayin da biyar suka ji rauni.
Bugu da kari, a cewar kafar jami'an tsaro, wani jami'in leken asirin sojan ya mutu a Benghazi, bayan da wani bom din da aka dasa a cikin wata mota ya tashi.
Wadannan tashe-tashen hankula na kara zama matsalar da Nuri Abusahmain, mutumin da aka zaba ranar Talata a matsayin sabon shugaban hukumar kolin harkokin siyasar kasar zai tunkara. (Ibrahim)