in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu za ta mayar da kaddarori ga Libya
2013-06-20 10:58:22 cri

A jiya Laraba 19 ga wata, shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya ce, kasar za ta mayar da kaddarori ga Libya wadda tsohon shugaban kasar Muammar Ghaddafi ya kai can, kamar yadda yake a tsarin MDD

Zuma wanda ya bayyana hakan ga majalissar dokokin kasar a Cape Town ya ce, hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da kasar ta cimmawa tsakaninta da Tripoli, inda wakilan kasar ta Libya suka gana tun da farko da ministan kudi Pravin Gordhan, domin bayyana bukatarsu na son a mayar musu da dukiyoyi da kaddarorin.

Yawan kudi ko kaddara da za'a mayar ga Libya dai ba'a san adadinsa ba, kuma shugaba Zuma ya ce, ba ya da masaniya ko kudin da kaddarorin mallakin tsohon shugaban kasar ne Ghaddafi ko kuma na gwamnatin kasar Libya.

Ana radedadin cewa, kaddarori da kudi na Libya a kasar Afrika ta Kudu za su kai dalar biliyan daya a tsabar kudi, zinarai da lu'u lu'u da aka ajiye su a tsakanin bankuna hudu da kuma kamfanonin harkar tsaro guda biyu.

An dai kiyasa cewa, tsohon shugaban kasar Libya Ghaddafi ya ajiye kaddarori na sama da dala biliyan 80 a kasashen duniya daban daban. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China