in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta jaddada niyyarta ta karfafa dangantaka da Libya
2013-06-05 12:15:54 cri

Game da takadama tsakanin Niamey da Tripoli da ta biyo bayan kalaman shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou na zargin kasar Libya da kasance wani sansanin 'yan ta'adda, hukumomin kasar Nijar sun jaddada niyyarsu na aiki kafada da kafada tare da hukumomin kasar Libya domin karfafa dangantakar zumunci da abokantaka dake tsakaninsu a fannonin daban daban, musammun a fannin yaki da ta'addanci da kisan kan iyaka.

Bayan hare-haren ta'addanci na ranar 23 ga watan Mayu a birnin Agadez da Arlit, shugaban kasar Nijar ya bayyana cewa, maharan sun fito daga kasar Libya, kalaman da faraministan kasar Libya Ali Zidane ya karyata tare da nuna cewa, kasarsa ba wani matsugunnin 'yan ta'adda ba ne.

A cikin wata sanarwa da ta fito a ranar Talata a birnin Yamai, a cewar ministan harkokin wajen kasar Nijar Bazzoum Mohamed, hukumomin kasar Nijar dake magana kan hare-haren ranar 23 ga watan Mayu, ba su neman su shafa ma hukumomin kasar Libya kashin kaji ko suna da hannu. Kasar Nijar ba ta neman yin matsin lamba kan kasar Libya, kawai illa ta nuna nauyin dake bisa kan gamayyar kasa da kasa, na taimakawa wata kasa abokiya domin fuskantar wata matsala da za ta iyar kasancewa barazana ga zaman lafiyarta a halin yanzu da kuma nan gaba, da ma makwabtanta, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China