A ranar Talata ne wani babban wakilin MDD ya bayyana cewa, dole ne a fuskanci 'yan matsaloli a shirin mika mulki a kasar Libya, to amma kuma kasar dake arewacin Afirka za ta amfana matuka daga zaman shawarwari dangane da inda za'a sa gaba.
Wakilin musamman na MDD na kasar Libya Tarek Mitri ya bayyana wa kwamitin sulhu na MDD cewa, kalubale a fuskar siyasa da tsaro da kasar ke fuskanta a yanzu, musababbinsu shi ne shekaru da dama da aka shafe karkashin mulkin danniya, rashin aikin kafofin gwamnati da kuma rudani dangane da al'adu na siyasa.
Shirin ba da tallafi ga kasar Libya na MDD UNSMIL, wanda Mitri ke jagoranta na ba da tallafi ga gwamnatin Libya da jama'ar kasar don a samu gudanar da sauyi na demokradiya, wanda aka tanada tun bayan hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi shekaru 2 da suka wuce.
Gaddafi ya shafe sama da shekaru 40 yana mulki a kasar ta arewacin Afirka har zuwa lokacin da aka yi juyin juya hali na demokradiya a shekarar 2011.
Mitri ya ci gaba da bayyanawa kwamitin sulhu cewa, akwai mutane kusan dubu 7 ko 8 a daure, mafi yawansu 'yan yankin Sahara na Afirka, wadanda kuma ake zargi mayakan Gaddafi ne, da a yanzu haka suna kan jiran a tuhume su ko a sake su.
Mitri ya ce, tsarin mika mutane dake tsare ga hukumomi abu ne dake kama da tafiyar hawainiya.
Da kuma yake zantawa da 'yan jarida bayan ganawar tasa da kwamitin sulhu, wakilin ya jaddada cewa, kasar Libya na matukar bukatar tallafi a bangaren siyasa daga kasa da kasa, ganin cewa, wasu daga cikin matsalolin kasar, kamar samar da tsaro a kan iyakoki, ba aiki ne da za ta iya gudanarwa ita kadai ba. (Lami)