Akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 56 suka samu rauni a hare-hare daban-daban da aka kai a wuraren shan shayi a kasar Iraki ranar Alhami, in ji 'yan sanda.
Wata majiyar 'yan sanda wacce ba ta son a san ko wanene ta baiyanawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua cewa, hare-haren da aka yi da bama-bamai daya bayan daya a wani shagon sayar da shayi a Baquba, babban birnin gundumar Diyala dake gabashin kasar Iraki, ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 10, kana 30 suka jikkata.
A halin da ake ciki kuma an kashe wasu mutane 2, kana 14 sun samu rauni a harin bom cikin wani kantin shayi a gundumar Adamiya dake arewacin Bagadaza, in ji majiyar, tare da karin cewa, mutane 12 sun samu rauni a wani harin bom a bakin hanya kusa da kantin shayi a gundumar Alforat dake kudu maso yammacin babban birnin kasar Iraki.
Babu wata kungiya da ta dau alhakin kai harin, to amma, a mafi yawan lokuta, kungiyar Al-Qaeda dake Iraki ita ce ke kai irin wadannan hare-hare na bom.
An saba samun harin bom a kasar Iraki, duk da cewa, an samu raguwar hakan tun bayan lokacin da lamarin ya yi kamari a shekarar 2006 da ta 2007, lokaci da kasar ta tsunduma cikin kasha-kashe na banbancin darika. (Lami)