in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi sassauci kan takunkumi da aka sanyawa Iraki dangane da mamaye Kuwaiti a 1990
2013-06-28 09:59:04 cri

A ranar Alhamis, kwamitin sulhu na MDD ya yi sassauci dangane da wasu takunkumi da aka dorawa kasar Iraki, inda kuma ya yi maraba da ci gaban da aka samu kan matakan warware batutuwan da suka shafi mamaya da kasar ta yi wa makwabciyarta kuma karamar kasar Kuwaiti dake yankin gabas ta tsakiya a shekarar 1990, gami da nemo 'yan kasar.

Wannan mataki yana kunshe ne cikin wani kuduri da kwamitin sulhun mai mambobi 15 ya zartas, wanda kuma aikinsa shi ne tabbatar da zaman lafiya da tsaro tsakanin kasa da kasa karkashin manufofin MDD.

Sabon mataki da kwamitin ya dauka na kira ga gwamnatin kasar Iraki ta ci gaba da neman 'yan asalin kasar Kuwaiti da ma kadarori, da suka bace tun lokaci da Saddam Hussein ya mamaye kasar a shekarar 1990, to amma kwamitin ya cire wasu sassa na tsofaffin kudurori kan wannan batu, wato kamar sashe na bakwai na tsohon kudurin wanda ya amince da yin amfani da karfin soja wajen aiwatar da matakan.

Bayan mamaya da Iraki ta yi wa kasar Kuwaiti, kwamitin ya kafa wata hukumar ba da diyya ta MDD (UNCC), wadda ke bayar da diyya ga wadanda lamarin ya janyowa hasara.

Izuwa watan Janairun bana, hukumar ta raba dalar Amurka biliyan 40.1 bisa bukatun hakan, wanda yawansu ya kai miliyan 1.5 daga wajen jama'a, hukumomi, gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa, inda yanzu dala biliyan 12.3 ne ya rage a biya. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China