in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu hare-hare a kasar Iraki sun hallaka mutane kimanin 23
2013-06-17 13:05:26 cri

Kimanin mutane 23 ne suka rasa rayukansu, yayin da kuma wasu 133 suka jikkata, sakamakon wasu hare-haren bam da aka dasa jikin wasu motoci, da kuma wasu harbe-harbe da bindigogi da suka auku a kasar Iraki a ranar Lahadi 16 ga watan nan.

Wannan dai hare hare na zuwa ne daidai lokacin da fadace-fadace tsakanin bangarorin da ba su ga maciji da juna ke kara tsananta, lamarin da ya sanya manzon MDD a kasar Martin Kobler, yin Allah wadai da hare-haren, tare da yin kira ga mahukuntan kasar, da su kira taron tattaunawa domin warware matsalolin dake addabar kasar, domin kaucewa afkawar kasar cikin karin mawuyacin hali.

Yankunan da bama-baman suka tashi dai sun hada da Al-Arousah dake yankin Basra, Nasriyah da Mahmoudiyah dake kudancin Bagadaza, da Aziziyah dake tsakiyar kasar, da kuma wata kasuwar saida kayan marmari dake Najaf, wato garin mabiya darikar Shi'a dake da tazarar kilomita 160 daga babban birnin kasar Bagadaza.

Ragowar wuraren da aka ba da rahoton fashewar bama-baman sun hada da garin Madain, da Mahawil, da kuma birnin Bagadaza, inda wata fashewa ta hallaka mutane 2, tare da jikkata wasu mutane 10.

An ce dai wani harin da aka kai kan wasu 'yan sanda da bindigogi ya haddasa mutuwar 'yan sandan 6, dake gadin wasu bututun danyan-mai a yankin Hatra, kudu da birnin Mosul. Har ila yau, rahotanni sun tabbatar da tashin wani bam a wani ginin ofishin 'yan sanda dake birnin Tuz-Khurmato, dake arewacin Bagadaza. Bugu da kari, wani babban jami'in sojin kasar Manjo Janar Ali Al-Frieji ya tsallake rijiya da baya, bayan tashin wani bam a bakin titi, yayin da yake wucewa cikin wani jerin gwanon jami'an tsaro, harin da nan take ya hallaka wasu masu tsaron lafiyarsa su 3.

Kawo yanzu dai, babu wata kungiya da ta dauki alhakin gudanar da wadannan hare-hare, ko da yake dai a kan danganta su da reshen kungiyar Al-Qaida dake kasar ta Iraki. A baya bayan nan dai, tashe-tashen hankula na sake dawowa a kasar ta Iraki, irin wadanda aka gani cikin shekarun 2006 da kuma 2007, lokacin da kasar ta auka cikin rigingimu masu nasaba da bangarorin al'ummarta da ba su ga maciji da juna. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China