A kalla mutane 27 ne suka rasa rayukansu yayin da guda 51 suka samu rauni, a daren ranar Alhamis, sakamakon tashin bom a wani kantin sayar da shayi dake Bagadaza, babban birnin kasar Iraki, in ji 'yan sanda.
Wata majiyar 'yan sanda ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua cewa, bom din ya fashe ne da misalin karfe tara da rabi na daren lokacin wajen, a unguwar Ameriyah dake yammacin birnin Bagadaza, kuma cikin wadanda suka mutu, akwai mata da kananan yara.
An samu karin tashe-tashen hankula a biranen kasar Iraki yayin da kasar ke shirin gudanar da zabe ranar Asabar mai zuwa, domin zaben mambobin majalisun yanki.
A kuma ranar Alhamis din da safe, an kashe a kalla mutane biyar a arewaci da tsakiyar kasar Iraki, ciki har da wani da ake kyautata zaton shugaban kungiyar Al-Qaida ne.(Lami)