Kafofin 'yan sanda sun bayyana cewa, mutane a kalla 12 ne suka mutu, kana 25 sun samu rauni yayin da 'dan kunar bakin wake ya tada bom a wani masallacin Shi'a dake Kirkuk a arewacin kasar Iraki ranar Alhamis.
Kafofin 'yan sanda da ba su so a san ko su waye ba sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua cewa, 'dan kunar bakin waken ya shiga masallacin Al Zahraa dake Kirkuk, mai nisan kilomita 250 daga Bagadaza, babban birnin kasar Iraki, inda ya tada bam dake jikinsa.
Fashewar bom din ya yi sanadin lalacewar masallacin, in ji kafofin, inda suka ba da karin bayani cewa, an kai harin ne lokacin da ake jana'izar wani da aka kashe a wani harin da aka kai ranar Laraba.
Tun da farko a ranar Alhamis din, an kai harin bama-bamai cikin mota da harbin bindiga a unguwannin 'yan Shi'a dake cikin Bagadaza da arewacin birnin Mosul, inda mutane a kalla 11 suka rasa rayukansu, kana 45 suka samu rauni.
Har ya zuwa yanzu, tashin hankali ba sabon abu ba ne a kasar Iraki, duk da samun raguwar hakan tun bayan masu tsanani da aka fuskanta a shekarar 2006 da ta 2007 lokacin da kasar ta tsunduma cikin yanayin kisa na banbancin akida. (Lami)