Majiyar 'yan sanda ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai ta Xinhua cewa, an samu fashewar bama bamai a daren Lahadi a garin Kirkuk dake arewacin kasar Iraqi inda suka yi sanadiyar rasuwar mutane goma sha daya sannan guda hamsin sun samu rauni.
An samu fashewar bama baman ne a sassa dabam dabam na garin, ciki har da wani massalacin 'yan Shi'a da kuma wani gidan rediyo, in ji majiyar da ba ya so a bayyana ko shi waye ba saboda ba shi da izinin yiwa 'yan jarida magana.
Ya bayyanawa Xinhua cewa, rahoto na karshe da aka samu na nunin cewa, mutane 11 ne suka rasu yayin da hamsin suka samu rauni, a hare-haren da suka kunshi tashin bama bamai a cikin motoci uku da kuma wasu bama bamai da aka dasa a gefen hanya har guda shida, gami da harin bindiga mai sulke.
Tuni dai jami'an tsaro suka kewaye wuraren da aka samu tashin bama baman saboda gudun fuskantar wasu hare-haren, in ji majiyar, to amma har yanzu babu wanda ya dau alhakin gudanar da hare-haren.
Garin Kirkuk dai yana da nisan kilomita 250 daga babban birnin kasar, Baghdad kuma yanki ne mai arzikin mai a arewacin Iraqi wanda kuma ake ganin yana daga cikin yankuna dake da dimbin rijiyoyin mai. Wannan yanki har ila yau yana cikin wuraren da ake takaddama kai tsakanin gwamnatin kasar da yankin Kurdistan, wacce take da 'yanci, amma ba cikakke ba na mulkin kai. Tun lokacin yakin iraki na shekarar 2003, ake samun tashin hankali a wannan yanki.(Lami)