A ranar Talata ne aka bude taron nazari kan aikin gona da abinci da zummar bullo da wata dabarar hada noman kayayyakin bukatun cikin gida da na fitar waje a Afrika a birnin Yamoussoukro dake tsakiyar kasar Cote d'Ivoire mai tazarar kilomita 230 da birnin Abidjan.
Jigon wannan taro shi ne 'wane nazari zai kawo taimako a Afirka da ke fama da kalubalen abinci?' Haka kuma taron zai mai da hankali musammun ma kan sakamakon nazarin da aka samu, dalilan matsalolin karancin abinci a shekarar 2008 da kimanta matakan da suka biyo. Hakazalika mahalarta taron za su tabo batun taimakon da tsarin sarrafawa ta hanyar noman auduga, habakar bukatun cimaka, ta yadda za'a tunkarar matsaloli ba tare da mantawa da taimakon kayayyakin abinci a cikin gida ba. Tattalin arzikin kasashen Afrika na dogaro yawanci da noma, kiwon dabbobi da kamun kifi. Matsalar karancin abinci ta kara tsananta tare da hauhawar farashin kayayyakin cimaka a shekarun 2007-2008, lamarin ya nuna cewa, ya kamata a kara samun kwarewa wajen bunkasa cigaban aikin noma, in ji Marcel de Raissac, mataimakin darekta janar kan nazari da dabaru a cibiyar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa kan aikin nazarin noma da cigaba (CIRAD). (Maman Ada)