in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zai yi wuya a gudanar da babban zaben Zimbabwe a watan Yuni, in ji wasu ministocin kasar
2013-04-18 10:54:03 cri

Minista mai lura da harkokin shari'a na kasar Zimbabwe Patrick Chinamasa, da takwaransa na ma'aikatar lura da harkokin masana'antu da cinikayya Welshman Ncube, sun bayyana shakkunsu kan yiwuwar gudanar da babban zaben kasar nan da watan Yuni dake tafe, kamar yadda shugaban kasar Robert Mugabe yake fatan ganin hakan.

Ministocin biyu sun bayyana tsarin gudanar da zaben, a matsayin babban kalubale ga burin da aka sanya gaba, amma ba wai himmar mahukunta ba. Ministocin biyu da suka fito daga jam'iyyun siyasar kasar mabanbanta, sun bayyana hasashen nasu ne a lokuta daban daban, inda ra'ayoyinsu don gane da lokaci mafi dacewa da gudanar zaben su ma suka banbanta.

Tun dai a baya shugaba Mugabe, ya bayyana burin gudanar da wannan zabe mai muhimmanci ga kasar a ranar 29 ga watan Yuni mai zuwa, yayin da shi kuma babban mai hamayya da shugaban, kuma firaministan kasar Morgan Tsangarai, ke bukatar a gudanar da zaben cikin watan Agusta, inda shi kuma ministan ma'aikatar lura da harkokin masana'antu da cinikayya Welshman Ncube, ke da ra'ayin kada kuri'u a watan Octoba mai zuwa.

Yayin zantawarsa da 'yan jaridu ranar Talatar da ta gabata, minista Chinamasa na jam'iyyar Zanu- PF mai mulkin kasar, ya bayyana cewa, kawo wannan lokaci, ba zai iya bayyana takamaiman lokacin da za a iya gudanar da zaben ba. Yayin da shi kuma a nasa bangare, ministan ma'aikatar lura da harkokin masana'antu da cinikayya Welshman Ncube, kuma jagoran jam'iyyar MDC dake cikin hadakar gwamnatin gambizar kasar ke cewa, bisa doka, wajibi ne a gudanar da zaben kasar kafin nan da 30 ga watan Octoba mai zuwa, ya kuma kara da cewa, abu ne mai wuya a iya gudanar da zaben, nan da 29 ga watan Yuni.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China