in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ta yi tir da harin da aka kaima ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a DRC
2013-05-09 14:11:44 cri

A ranar Laraba 8 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ta yi suka da babbar murya dangane da harin da aka kai ma jami'an soji dake aiki tare da ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na majalissar a ranar Talatan wannan makon a kasar jamhuriyar demokradiya ta Kongo DRC, abin da ya yi sanadiyar mutuwar ma'aikaci daya.

A cikin wata sanarwar da kwamitin mai mambobi 15 ta fitar, ta yi matukar Allah wadai da harin da aka yi, musamman tare da kokarin yin garkuwa da ma'aikatan da wadansu 'yan bindiga suka yi ma tawagar sojin daga garin Walungu zuwa Bukavu a kudancin Kivu a ranar Talatan da ta gabata, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya, 'dan asalin kasar Pakistan, tana mai mika ta'aziyarta ga iyalan wannan mamacin, gwamnatin kasar Pakistan da kuma rundunar kiyaye zaman lafiyar ta majalissar dake kasar ta DRC MONUSCO.

Kwamitin ya kuma bukaci gwamnatin DRC da ta hanzar ta cafko wadanda suka aikata wannan danyen aiki, tare da gurfanar da su a gaban kuliya, a cewar sanarwar da ta fitar, mambobin kwamitin sun kara jaddada muhimmancin dake akwai na inganta matakan da aka tsara na samar da kariya ga ma'aikatan wanzar da zaman lafiya ga dukkan jami'an tsaro da suka hada da sojoji, 'yan sanda, masu sa ido a kan ayyukan soji da kuma ma'aikatan da ba su dauke da makamai na MONUSCO da aka kai domin aiwatar da ayyukan majalissar yadda ya kamata.

A wata sanarwar tun da farko da kakakin magatakardar MDD Martin Nesirky ya fitar, ya sanar da damuwa da kuma matukar jimamin magatakardar Ban Ki-moon game da wannan harin da aka kai wanda ya yi sanadiyar mutuwar 'dan kasar Pakistan, yana mai bayyana cewa, wannan ya zama wani laifin yaki.

Gabashin jamhuriyar demokradiya na Kongo yana fuskantar tashe-tashen hankali na tsawon watanni tun bayan da wata sabuwar kungiyar 'yan tawaye mai suna M23 suka bayyana suka fara kai hare-hare a arewacin Kivu a farkon shekarar bara.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China