Shugabanni bakwai na kungiyar tattalin arzikin kasashen dake tsakiyar Afrika (CEEAC) da na kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS sun isa birnin Yaounde na kasar Kamaru tun ranar Lahadi domin halarta babban taro na kwanaki biyu kan batutuwan kiyaye tsaro a yankin tekun Guinee da za'a bude ranar Litinin a karkashin jagorancin MDD. Shugabannin kasashe kamar su Mahamadou Issoufou na Nijar, Goodluck Ebele Jonathan na Nijeriya, Manuel Pinto da Costa na Sao Tome-Principe, Teordoro Obiang Nguema Mbasogo na Guinee-Equatoriale, Thomas Boni Yayi na kasar Benin, Blaise Compaore na Burkina-Faso da kuma Denis Sassou Nguesso na kasar Congo-Brazaville sun isa babban birnin kasar Kamaru domin wannan taro, tare kuma da mataimakiyar shugaban kasar Gambia, madam Isatou Njie Saidou. A cewar wata majiya mai tushe daga hukumomin kasar Kamaru, sauran shugabanni kamar su Ali Bongo Ondimba na kasar Gabon, Idriss Deby Itno na kasar Chadi da Alassane Ouatttara na kasar Cote d'Ivoire za su isa ranar Litinin da safe a kasar ta Kamaru. (Maman Ada)