in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya isa kasar Kamaru
2013-03-25 10:15:48 cri

Wata majiyar kamfanin dillancin labaru ta ma'aikatar tsaron kasar Kamaru, ta tabbatar da cewa, shugaba Francois Bozize ya sauka a gabashin kasar ta Kamaru, bayan tserewarsa daga birnin Bangui, biyowa bayan kwace birnin da dakarun Seleka suka yi a ranar Lahadi 24 ga wata.

Majiyar ta ce, wani jirgi mai saukar ungulu dake da shugaba Bozize ya sauka a karamin filin saukar jirage dake Batouri, da misalin karfe 6 na maraicen ranar Lahadi. Bayanai daga fadar shugaban kasar ta tabbatar da cewa, Bozize ya fice ne da kimanin rabin sa'a, kafin dakarun Seleka suka samu nasarar kai hari ga fadar.

Cikin watan Janairun da ya gabata ne dai shugaba Bozize, da kungiyar 'yan tawayen na Seleka suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar sulhu a birnin Libreville na kasar Gabon, kafin daga bisa Selekan ta bai wa bangaren gwamnati wa'adin aiwatar da wannan yarjejeniya. Bayan shudewar wannan wa'adi ne kuma maharan kungiyar suka sake jan daga, tare da kai hare-hare kan dakarun gwamnati, bisa zargin da suka yi wa gwamnatin, na kin martaba waccan yarjejeniya, musamman ma batun shigar da dakarunta cikin rundunar sojin kasar, da kuma ficewar sojojin Afirka ta Kudu da Uganda daga kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China