in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira da a kara zuba jari domin bunkasa aikin yi a Afrika
2013-06-18 10:44:39 cri

Shugabar kwamitin kungiyar tarayyar Afrika AU, dokta Nkosazana Dlamini Zuma, ta yi kira a ranar Litinin a birnin Geneva wajen kara zuba jari, ta yadda za'a taimaka wajen samar da aikin yi, domin kai ga samun bunkasuwa da kawar da talauci a Afrika.

'Mun dauki niyyar kara yawaita kokarinmu domin taimakawa samar da aikin yi, da dukufa wajen kawar da talauci, samar da bunkasuwa da damar rarraba arzikin kasashenmu cikin adalci, musammun ma ga mata da matasa.' in ji madam Zuma a yayin taron kasa da kasa na kwadago dake gudanarwa tun daga ranar 5 har zuwa 21 ga watan Yuni a Geneva.

'Nahiyar Afrika ta jurewa rikice-rikice na cikin gida da waje da kyau, don haka za ta cimma bunkasuwa da kashi 4.8 cikin 100 a shekarar 2013, kana da kashi 5.3 cikin 100 a shekarar 2014.' in ji madam Zuma tare da bayyana cewa, nan da shekaru 50, Afrika za ta kunshi ma'aikata biliyan 1.1 ke nan fiye da kashi daya cikin uku ta fuskar kwadago a duniya.

Jami'ar ta yi kira da a kara zuba jari a Afrika a cikin fannonin kayayyakin more rayuwar jama'a, noma, kanana da manyan masana'antu, sufurin jiragen ruwa, makamashi, fasahohin sadarwa da labarai da yawon bude ido.

'Haka kuma ya kamata mu kara zuba jari a cikin harkokin cimaka, kiwon lafiya da ilmi domin amfanawa mutanen kasashenmu da kuma ba su damar samun kwarewa, ta yadda za su kawo nasu taimako ga cigaban al'umma.' in ji madam Zuma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China