A ranar Litini ne ministan harkokin waje na kasar Faransa Laurent Fabius ya nuna kyama dangane da nuna hotunan bidiyo masu tayar da hankali na 'yan kasar Faransa guda bakwai da aka sace a makon da ya wuce, wanda shi ne irinsa na farko tun bayan sace su da aka yi.
Fabius ya ce, 'yan kungiyar Boko Haram sun sanya hotunan bidiyo na iyali 'yan asalin Faransa da aka sace ranar Talata da ta wuce a kasar Kamaru kan shafinsu na intanet.
Ya ce, hotunan sun ta da hankali matuka kuma sun nuna yadda ake cin zarafin mutanen.
A wani takaitaccen hoton bidiyo da aka sanya kan shafin intanet na YouTube a ranar Litini, wasu 'yan bindiga su uku dake ikirarin cewa, su 'yan kungiyar Boko Haram ne su zagaye mutanen da aka sace, ciki har da yara guda uku, suna barazanar za su kasha su muddin jami'an kasar Najeriya da na Kamaru ba su saki mayakan kungiyar ba,
Babban jami'in ma'aikatar harkokn wajen na Faransa ya ce, ana kokarin tabbatar da gaskiyar hotunan bidiyon.
A halin da ake ciki, fraministan Faransa, Jean-Marc Ayrault bayan wata ganawa da aka yi ta musamman kan tsaro ya tabbatar da cewa, kungiyar ta Islama ce ta sace mutanen tare da karin cewa, kila mutanen da aka sace suna nan boye a Najeriya.
Jama'a da kuma cibiyoyin kasar Faransa sun shiga yanayin barazana bayan da Paris ta dau matakin tura sojojinta zuwa kasar Mali don fatattakar 'yan tawayen masu tsatsauran ra'ayin Islama daga arewacin kasar.
Zuwa yanzu, 'yan kasar Faransa guda 14 ne ke hannun kungigoyi dake da alaka da kungiyar Al-Qaeda a yankin Sahel.(Lami)