in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan halartar babban taro kan batun Sham
2013-05-27 16:49:42 cri
A ranar Litinin 27 ga wata, a gun taron manema labaru da aka shirya a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, Sin na fatan halartar babban taro kan batun Sham, domin yin kokari tare da bangarori daban daban, da zummar sa kaimi ga daidaita batun kasar ta Sham cikin adalci da lumana.

A kwanan baya, kasa da kasa sun kara yin mu'amala tsakaninsu kan babban taro dangane da batun Sham da Rasha da Amurka suka kira. Mr Hong wanda ya fadi haka a yayin da yake amsa tambayar manema labarai dangane da ra'ayin kasar Sin kan wannan taro, da kuma ko Sin za ta halarta? Ya kuma yi bayanin cewa, Sin tana nuna goyon baya ga duk kokarin da aka yi wajen daidaita batun Sham a siyasance, tare da maraba da kirar da aka yi na yin wannan taro.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China