Bisa labarin da aka bayar, an ce, Berhane Gebre-Christos ya yi imani cewa, kogin nil zai zama tamkar wata gada don inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Habasha da Masar, amma a sa'i daya kuma, ya bayyana cewa, yana fatan Masar za ta girmama hakkin raya albarkatun da Allah ya fuwace wa kasar Habasha.
Domin gina wata madatsar ruwa mai suna Renaissance da za ta samar da wuta megawatt dubu 6, kwanan baya, kasar Habasha ta fara yin gyare-gyare game da sassan hanyoyin kogin Nil, abin da ya kawo damuwa daga kasar Masar game da albarkatun ruwa na kasar. Game da matakin da kasar Habasha ta dauka, shugaban kasar Masar Mohamed Morsi ya bayyana cewa, 'Idan akwai bukata, za mu yi amfani da jininmu don kiyaye kogin Nil.''
Bisa yarjejeniyar da aka daddale a tsakiyar karnin 20, an ce, kasar Masar da makwabtarta Sudan suna da hakkin yin amfani da kogin Nil, amma sauran kasashen da kogin Nil ya malala ya bi su sun bayyana cewa, wannan yarjejeniya ba ta dace da bukatun samun bunkasuwa na zamani ba. (Bako)