in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire da Ghana sun kafa cibiyoyin samar da bayanai domin saukaka kasuwanci tsakaninsu
2013-05-29 10:02:38 cri

Cibiyoyin samar da bayanai ne aka kafa a kan iyakar dake raba Cote d'Ivoire da Ghana domin saukaka musanya da kasuwanci tsakanin kasashen biyu, a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu daga wasu majiyoyin ma'aikatar harkokin sufurin kasar Cote d'Ivoire a ranar Talata.

A cewar babban darektan ofishin dakon kaya na Cote d'Ivoire, Fako Kone, bude wadannan cibiyoyin samar da bayanai kan iyaka na Noe a kasar Cote d'Ivoire da Elibo a kasar Ghana na daya daga cikin bukatun da cibiyar yammacin Afrika kan kasuwanci ta gabatar, a cikin shirin kimantawa na tsarin kawar da shingen kasuwanci a shiyyar kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS.

Wata dama ce ta samar da bayanai ga manyan 'yan kasuwa da masu kai da kawo, musammun ma bisa dokokin kasuwanci na shiyoyi da sharudan hukumomin kan iyaka, domin rage yawan kashe kudi da wa'adi, ta yadda za'a taimakawa bunkasa yawan kayayyakin musanya kan iyakoki, in ji mista Kone.

Tun daga watan Agustan shekarar 2011, cibiyoyin samar da bayanai kan iyaka suka bude a yawancin kan iyakokin kasashen mambobin kungiyar ECOWAS. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China