in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaro na MDD ya kara tsawon lokacin aikin hukumominsa biyu a Libya
2013-03-15 09:59:17 cri

Kamitin tsaro na MDD ya tsayar da wani kuduri ranar Alhamis din nan dangane da kara yawan lokacin aikin hukumar ba da tallafi ga kasar Libya ta MDD (UNSMIL) da shekara daya, kana rukunin kwararru masu lura da takunkumi da aka dorawa kasar Libya, su ma an kara masu watanni 13.

Hukumar ta MDD dake aiki a Libya, an kafa ta ne a watan Satumban shekarar 2011, don maido da tsaron jama'a da kuma farfado da tattalin arzikin kasar dake yankin arewacin nahiyar Afirka cikin watanni uku, kana kwamtin tsaro na MDD ya kuma dorawa hukumar ta UNSMIL aikin taimakawa gwamnatin kasar a fuskar bunkasa kiyaye doka, kyautata kiyaye 'yancin bil adama da kuma maido da tsaron jama'a.

Wa'adin wannan aiki da aka damkawa hukumar karkashin jagorancin wakilin musamman na magatakardan MDD, zai kare ne ranar 16 ga watan Maris.

A halin da ake ciki kuma kwamitin tsaro na MDD mai mambobi guda 15 ya bukaci rukunin kwararru wadanda su ma aikinsu zai kare ranar 17 ga watan Maris da su taimaka wa gwamnatin kasar Libya wajen shawo kan bazuwar miyagun makamai da dai makamantansu, musaman ma kanana da manyan makamai, da ma makaman kakkabo jiragen sama, kana su tabbatar da tsaro da kuma gudanarwa a kan iyakokin kasar, in ji kudurin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China