A ranar Alhamis ne kasashen Sudan, Masar da Libya suka cimma yarjejeniyar karfafa hadin gwiwa a bangaren albarkatun ma'adinai don biyan bukatun tattalin arzikin kasashen uku.
A ranar ta Alhamis ce aka fara tattauna tsakanin kasashen uku a birnin Khartoum a bangaren hako ma'adinai, ganawar da ta samu halartar ministan ma'adinan kasar Sudan Kamal Abdullatif, ministan man fetur da albarkatun ma'adinai na kasar Masar Osama Kamal da kuma ministan masana'antu na kasar Libya Suleiman Ali Al-Fitory.
Taron ya tattauna batun kafa asusun hako ma'adinai na hadin gwiwa don daukar nauyin ayyukan hako ma'adinai a kasashen na Larabawa ta hannnun kawancen kasashen Larabawa tare da gudanar da nazari don gano hanyoyin da suka dace na hako albarkatun ma'adinai.(Ibrahim)