in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Somaliya ta ce, hana zirga-zirgar jiragen MDD gurguwar shawara ce
2013-05-20 11:01:37 cri

Gwamnatin kasar Somaliya a jiya Lahadi ta ce, gurguwar shawara ce ga kananan hukumomi dake arewacin yankin da suka balle suka koma yankin Somaliland, na hana jiragen MDD sauka a yankinsu, sannan kuma suka hana wadanda suka riga suka sauka su tashi a filin jiragen samansu.

Mahukunta a yankin Somaliland dai sun hana jiragen saman MDD su sauka, sannan wadanda ke nan tashi a filin jiragen sama dake garuruwan Hargeisa da kuma Berbera, in ji ministan yada labarai na kasar Somaliya Abdullahi Hersi.

Ya yi bayanin cewa, wannan yanki ya yi hakan ne wai domin mai da martanai game da daftarin amincewa juna tsakanin Somaliya da hukumar zirga-zirgan jiragen sama na MDD wadda ke da zama a kasar Kenya suka sanya ma hannu, wanda a hankali yake ba da karfin ikon filayen jiragen saman ga gwamnatin kasar Somaliya mai fadar gwamnati a Mogadishu.

Tuni dai gwamnatin kasar Somaliya ta mika sakon ban hakuri ga MDD saboda wannan mataki da wannan yanki na Somaliland suka dauka, suna mai bayyana shi a matsayin karya alkawarin na dokar kasa da kasa da kuma keta hakkin ikon MDD da na ma'aikatar ta wadanda suke kasar domin su taimaki al'ummar kasar ta Somaliya.

Gwamantin kasar Somaliya har ila yau ta lura tare da nuna yabawarta a kan muhimmancin kayayyakin taimako da MDD da sauran bangarorinta ke ba su. Sannan kuma, a cewarta, karbe ikon filayen saukan jiragen sama ba maganar da ya shafi siyasa ba ne, don haka abu ne da ya kamata a daidaita don gyara a inda ake da matsala game da amfani da sararin samaniyar kasar, sannan kuma duk wata tattaunawa game da hakan sai dai a yi ta a cikin ka'idar ikon mulkin kai ta Somaliya.

Yankin Somaliland dai ya yi ikirarin samar da 'yancin kansa a shekarar 1991 daga cikin Somaliya, sai dai kasashen duniya ba su amince da wannan yanki ba a hukumance, don haka kasar Somaliya kawai ake mara ma baya mai babban birni a Mogadishu.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China