Kasar Isra'ila za ta taimakawa cigaban karkara a kasar Cote d'Ivoire ta hanyar horar da daliban kasar a fasahar noma ta zamani, a wani labari da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu a ranar Lahadi daga cibiyar jami'ar aikin noma ta Houphouet-Boigny (INP-HB) dake Yamoussoukro a tsakiyar kasar mai tazarar kilomita 230 da birnin Abidjan.
A cewar darektan INP-HB, Koffi N'Guessan, kasar Isra'ila ta gudanar a cikin tsarin "karatun noma" da wata jarrabawa domin zaben kwararrun daliban dake jami'ar aikin noma ta kasar INP-HB da makarantar aikin noma dake Bingerville dake birnin Abidjan.
Bisa wannan tunani na jakadan kasar Isra'ila dake kasar Cote d'Ivoire, wadannan dalibai da 'yan makaranta za su je kasar Isra'ila domin samun horo a kan wasu fannonin aikin noma da kiwo a tsawon watanni goma sha daya.
Nahiyar Afrika na bukatar irin wannan horo ga dalibanta domin cimma nasarar mai da filayen da ba'a samun ruwa zuwa wuraren noma kamar yadda Isra'ila ta yi, in ji mista Koffi N'Guessan. A cewarsa, wadannan dalibai za su dawo kasar Cote d'Ivoire domin taimakawa cigaban noma ta hanyar horar da mutanen karkara, ta yadda za su amfani da aikin noma. (Maman Ada)