in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nan da 2016 sabon filin hakar danyan mai na Ghana zai samar da ganga dubu 76 kowace rana
2013-04-24 14:21:40 cri

Hukumar lura da harkokin man fetir da iskar gas ta kasar Ghana, ta ce, mahakar iskar gas, da danyan mai ta kasar dake "Tweneboa Enyenra da Ntomme", za ta rika samar da danyan mai da yawansa ya kai ganga dubu 76, tare da mizanin iskar gas miliyan 50 a kowace rana, idan ta fara cikakken aiki nan da shekara ta 2016. A cewar shugaban kamfanin lura da harkokin man fetir na kasar Nana Boakye Asafu-Adjaye, ana sa ran fara wannan aiki ne cikin wannan shekara, yayin da kuma ake fatan fara fidda danyan mai daga wurin da farkon shekarar 2016.

Cikin jawabinsa na bude taro karo na 4, na nune-nunen albarkatun mai da iskar gas da aka gudanar a kasar ta Ghana, Asafu-Adjaye ya bayyana cewa, baya ga wannan aiki, shi ma filin hakar mai na Sankofa da Gye-Nyame, dake Tano, za a fara aikinsa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017, aikin da kamfanin kasar Italiya "ENI" zai gudanar. Tuni dai mai magana da yawun wani kamfanin hakar mai mai suna "Tullow oil" na kasar Birtaniya George Cazenove, ya bayyana cewa, kamfaninsu ya mika bukatar aiwatar da aikin filin Tweneboa Enyenra da Ntomme, a farkon watan nan da muke ciki, suna kuma dakon amsa daga mahukuntan kasar.

Kasar Ghana dai na burin kafa wata cibiyar bunkasa kasuwanci da cinikayyar albarkatun mai, wadda za ta habaka harkokin kasuwanci a wannan sashe, domin kasar ta zamo a sahun gaba, wajen samar da ingantattun ayyuka, da kayan sarrafawa a fannin, matakin da mahukuntan kasar ke ganin zai haifar da karuwar ayyukan yi, da bunkasar tattalin arziki tun daga tushe.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China