in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Ghana ya gana da jami'in majalissar CPPCC
2013-05-29 10:17:55 cri

A ranar Talata 28 ga watan nan ne mataimakin shugaban kasar Ghana Kwesi Bekoe Amissah-Arthur, ya gana da mataimakin shugaban majalissar ba da shawara, kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin Ma Biao a ofishinsa.

Yayin ziyarar tasa, mataimakin shugaban majalissar ta CPPCC ya mika sakon kyakkyawan fatan jagororin kasar Sin ga al'umma, da shuwagabannin kasar ta Ghana, yana mai jaddada irin alaka mai dadadden tarihi dake tsakanin kasashen biyu. Mao Biao ya ce, kasar Sin na dora muhimmancin gaske, ga huldar abokantaka dake tsakaninta da Ghana, tare da fatan ziyarar tasa za ta dada bunkasa hadin kai da cudanya mai ma'ana dake tsakanin bangarorin biyu.

A nasa jawabi, mataimakin shugaban kasar ta Ghana ya bayyana godiya ga kasar Sin, bisa irin tallafin da take baiwa kasarsa ta fuskar bunkasa tattalin arziki, da yanayin zamantakewar al'ummar a tsahon lokaci. Amissah-Arthur ya kara da cewa, kasashen biyu, sun dauki lokaci mai tsaho suna gudanar da huldodi da suka kawowa junansu alherai. Daga nan sai ya yi fatan dorewar irin wannan dangantaka daga dukkanin fannoni, tsakanin bangarorin biyu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China