in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta yi hasashen samun ciniki daga man fetur na dalar Amurka miliyan 581 bana
2013-03-12 14:31:50 cri

Kasar Ghana ta yi wani hasashen samun ciniki daga harkokin man fetur na dalar Amurka miliyan 581 cikin wannan shekara, in ji wani jami'in kasar a ranar Litinin a birnin Accra.

Darektan kula da wannan fanni a ofishin ministan kudin kasar Ghana, Idrissu Alhassan ya sheda wa manema labarai cewa, an yi hasashen ne bisa tushen daidaituwar dake rinjaye bisa shekaru bakwai, kamar yadda dokar dake kula da harkokin cinikin man fetur ta kasar wato PRMA ta tanada.

Wadannan alkaluma na auna madaidaicin farashin gurbataccen man fetur bisa dalar Amurka 94,36 kowace ganga, da samar da gangar man fetur 83,341 kowace rana, bisa tushen daidaicin karuwa bisa shekaru uku.

Mahakar Jubilee na samar da karin mai a halin yanzu na kimanin gangar man fetur 115 kowace rana, haka kuma ayyukan gina wasu sabbin rijiyoyin samar da wani karin wannan makamashi sun fara samar da sakamako mai kyau a watannin ukun baya na shekarar 2012.

A shekarar 2011 ta kasance shekarar farko ga gasar Ghana wajen samun cike aikin sarrafawa, haka kuma cinikin man fetur ya cimma jimillar dalar Amurka miliyan 444,12, wadda ta haura ga dalar Amurka miliyan 541,07 a shekarar 2012. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China