in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutum 1 ya rasu sakamakon hatsaniya kan batun mallakar fili a Ghana
2013-03-13 10:30:55 cri

Rundunar 'yan sanda reshen yankin Tamale mai nisan kilomita 658 daga birnin Accra na kasar Ghana, ta tabbatar da rasuwar mutum guda, yayin da kuma wasu da dama suka samu raunuka daga harbin bindiga, biyowa bayan wani tashin hankali da ya barke tsakanin wasu al'ummun yankin 4, don gane da batun mallakar wani fili.

Da yake zantawa da manema labaru, mai magana da yawun rundunar na yankin arewacin kasar, mataimakin sifirtandan 'yan sanda Ebenezer Tetteh, ya ce, sun samu rahoton rasuwar wani mutum mai suna Mumuni Dramani, 'dan shekaru 40 da haihuwa, sakamakon harbin bindiga da ya samu, kuma tuni aka garzaya da gawarsa wani asibitin koyarwa dake garin Tamale.

Bisa aukuwar wannan lamari, hukumar 'yan sandan kasar ta cafke mutane 21 da ake zargi da hannu cikinsa, an kuma gano wasu tarin makamai, ciki hadda bindigogi da albarusai, da kayan sarki, daga wata maboya. Haka nan rundunar ta matsa kaimi wajen sanya ido kan wannan yanki, domin kaucewa sake aukuwar abin da ya faru.

Bugu da kari, jagororin al'ummun Dagomba biyu, wadanda ke makwaftaka da yankin Kumbaom-Naayili, sun fara tattaunawa kan musabbabin aukuwar wannan balahira, domin kawo karshen zaman dar-dar.

Shi dai wannan riciki da kan auku kusan kowace shekara a wannan yanki, na daukar sabon salo a lokuta mabambanta, tun dai shekara ta 1985, lokacin da al'ummun wannan yanki na Tamale suka fara yin fito-na-fito da junansu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China