Wasu 'yan bindiga 4 sun rasa rayukansu, yayin wani dauki ba dadi da ya auku, tsakanin jami'an rundunar hadin gwiwa ta soji da 'yan sandan Nigeria da 'yan bindigar, a rukunin gidajen Alu dake unguwar Bado ta jihar Sokoton Nigeria.
Kwamandan rundunar hadin gwiwar Birgediya-Janar Mohammed Tasi'u ne dai ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, a ranar Laraba 13 ga watan nan. A cewarsa, cikin 'yan bindigar da aka harbe, hadda wata mace guda daya. Shi ma a nasa bangare, kwamishinan 'yan sandan jihar Shu'aibu Gambo, ya shaida wa manema labaru cewa, an samu nasarar kwato makamai da dama daga 'yan bindigar, ciki hadda bindigogi da harsasai da kuma motoci guda biyu.
Wannan simame, a cewarsa, ya biyo bayan tsaigunta mafakar wadannan bata gari, da aka yi wa jami'an tsaron. Tuni dai aka rushe gidan da maharan suke fakewa bayan aukuwar simamen.(Saminu)