in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya nemi hadin kan Libya dangane da hari a Benghazi
2013-03-14 09:41:24 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama a ranar Laraba ya yi alkawarin ba da hadin kai ga kasar Libya a yanayin sauyi da take ciki tare da jadadda samun goyon bayan kasar dake yankin arewacin Afirka, dangane da hukunta wadanda suka kai hari a ofishin jakadancin Amurka dake Benghazi.

Wata sanarwa daga mai magana da yawun majalisar tsaron kasar Amurka Caitlin Hayden ta bayyana cewa, shugaban ya shigo wata ganawa ne a fadar 'white house' dake kankama tsakanin babban mai ba shi shawarwari kan tsaro Thomas Donilon da fraministan Libya Ali Zeidan, wanda ke ziyarar farko a birnin Washington.

Obama ya sake jadadda aniyarsa na ganin an hukunta wadanda suka kai hari a ofishin jakadancin Amurka dake Benghazi ranar 11 ga watan Satumbar bara, kana ya kuma nuna muhimmancin samun hadin kan kasar Libya kan bincike da ake gudanarwa.

A yayin harin, an kashe jakadan Amurka Christopher Stevens da wasu wakilan Amurka guda uku, inda kuma lamarin ya zamo abin da aka yi cece-kuce a kansa yayin yakin neman zaben shekarar 2012 wato lokaci da 'yan jam'iyyar Republicans suka yi suka kan gwamnatin Obama dangane da ba da bayani masu sabani da juna, wato da farko suka ce, harin ya auku ne dangane da zanga-zangar kin jinin Amurka, dayan kuma aka ce, wai hari ne na 'yan ta'adda.

A ganawar tasu, Obama ya bayyana wa Zeidan cewa, ya zabi Deborah Jones wacce fitacciya ce a aikin ofishin jakadanci, ta zama jakadar Amurka a kasar Libya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China