Jiya ranar 9 ga wannan wata, wani jami'in ma'aikatar kula da harkokin gidan kasar Iraki ya bayyana cewa, a daren wannan rana, boma-bomai cikin motoci sun fashe har sau hudu a Bagadaza, babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 16 yayin da 77 kuma suka ji rauni.
Wani jami'in kula da harkokin cikin gidan kasar da bai fayyace sunansa ba ya nuna cewa, a wannan rana da dare, boma-bomai a cikin motoci sun fashe a wasu unguwoyin 'yan shi'a hudu dake cibiyar birnin Bagadaza har sau hudu, hare-haren da suka haddasa mutuwar 16 tare da raunana 77.
Ban da wannan kuma, a ranar da dare, an kai hari ga sojojin yankin Abu Ghrab dake nisan kilomita 25 daga yammacin birnin Bagadaza. Wasu masu dauke da makamai da ba a san asalinsu ba sun kai hari ga wata tashar bincike, sun harbi sojoji uku a ciki har lahira. Daga baya, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar sun yi musanyar wuta da wadannan 'yan bindiga, tare da kashe biyu dake cikinsu har lahira tare da kama wani daban, kana sauran masu dauke da makamai sun arce, sojojin kiyaye zaman lafiya suna kokarin neman kama su.
Kasar Iraki ta sake gamuwa da hare-haren ta'addanci har sau ashirin a wurare daban daban na kasar, wadanda suka salwanta rayuwar mutane a kalla 52 yayin da 184 suka ji rauni, yawancinsu sojojin kiyaye zaman lafiya da musulmai na rukunin Shi'a ne. Har yanzu, babu kungiya ko mutum da suka sanar da daukan alhakin wadannan hare-haren ba.(Jamila)