Bugu da kari, gwamnatin kasar ta Sham ta ce, wannan matakin da shugaba Morsi ya dauka ba wani abu ba ne, illa aiwatar da manufofin kungiyar nan ta 'yan uwa musulmi ko "Muslim Brotherhood" a turance.
Da yake tsokaci kan wannan batu, ministan watsa labarun kasar Sham Omran al-Zoubi cewa ya yi, tuni ya dace shugaba Morsi ya dauki makamancin wannan mataki na yanke huldar diplomasiyya da kasar Isra'ila, wadda a cewarsa ke ci gaba da kisan Palasdinawa.
Wannan dai mataki da mahukuntan kasar ta Masar suka dauka, tare da ragowar masu adawa da gwamnatin kasar ta Sham, na zuwa ne daidai lokacin da rundunar sojin kasar ta Sham ke samun gagarumin rinjaye kan 'yan adawa a sassan kasar daban daban.(Saminu)