Dangane da wannan, a lokacin da Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin yake amsa tambayoyin manema labaru a nan Beijing a ran 28 ga wata, ya ce, abun gaggawa da za a yi shi ne sa kaimi kan gwamnatin Sham da masu adawa da ita da su yi shawarwarin siyasa da kuma kaddamar da shirin shimfida wani tsarin siyasa na wucin gadi cikin hanzari bisa sanarwar taron ministocin harkokin waje da kungiyar kula da batun Sham ta shirya a birnin Geneva. (Tasallah)