in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar da ke mulki a Sudan ta bukaci Juba da ta daina goyon bayan 'yan tawaye
2013-05-13 10:39:03 cri

A ranar Lahadi 12 ga wata ne jam'iyyar NCP da ke mulki a Sudan ta bukaci gwamnatin Sudan ta Kudu da ta daina goyon bayan 'yan tawayen da ke yakar gwamnati a Khartoum, sannan su daina baiwa shugabannin 'yan tawayen mafaka.

Kakakin bangaren siyasa na jam'iyyar NPC Yasir Yousif, ya bayyana wa manema labarai a ranar Lahadi cewa, goyon bayan da gwamnatin Juba ke baiwa 'yan tawaye, ya gurgunta yunkurin aiwatar da yarjeniyoyin hadin gwiwa da aka cimma da Sudan ta Kudu.

Yasir ya ce, babu tantama za a tattauna batun goyon bayan da Juba take baiwa 'yan tawayen a taron kolin da shugaba Omar al-Bashir zai yi da takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir, yayin da ya iso Khartoum.

Ya kuma nanata cewa, Khartoum ba za ta sasanta da kungiyar SPLM, bangaren arewaci ba, wadda ke yakar gwamnatin Sudan a yankunan kudancin Kordofan da Blue Nile, har sai sojoji sun yake su tare da 'yantar da yankunan Sudan.

Tun a shekara ta 2011 ne bayan da Sudan ta Kudu ta samu 'yanci, jihohin Kordofan ta kudu da Blue Nile suke ta fuskantan arangama tsakanin sojojin Sudan da mayakan SPLM bangaren arewaci.

Gwamnatin Khartoum dai ta fara zargin Juba ne, bayan da aka samu ingantuwar dangantaka tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, bayan da sassan biyu suka sanya hannu kan yarjejeniyar inganta matakan tsaro a kan iyakokin kasashen biyu, batun mai, cinikayya da sauran batutuwa a ranar 8 ga watan Maris a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China