Dubun dubatar jama'a ne yau suka yi tururuwa a fadar mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero domin sheda bikin cikar sa shekaru 50 kan karagar mulkin masarautar Kano da kuma bikin cikarsa shekaru 83 da haihuwa.
Tsoffin shugabannin tarayyar Najeriya Janaral Abdulsalami Abubakar da Janaral Muhammadu Buhari na daga cikin mutanen da suka halarci bikin, wanda a lokacin aka gudanar da wata kasaitacciyar Durba.
Sauran wadanda suka halarci bikin sun hada da gwamnonin jahohin Edo Adams Oshiomole da na Sokoto Aliyu Magatakardan wammako da mai masaukin bakin su gwamnan Kano Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso da sarkin musulmi Sa`ad Abubakar da daukacin sarakunan arewaci dana kudancin Najeriya.
A jawabinsa, mataimakin shugaban kasa Arch. Namadi Sambo ya bayyana sarkin Kano Alhaji Ado Bayero a matsayin jarumin sarki mai son cigaba tare da hadin kan al`ummar Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa wanda ya wakilci shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya tabbatar da cewa, gwamnatin Tarayya za ta cigaba da baiwa sarakunan kasar cikakken hadin kan da ya kamata.
Shi ma da yake jawabi, gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi`u Musa kwankwaso ya ce yana samun karin ilimi matuka a zaman da yake yi da sarkin na Kano, ya tabbatar da cewa, akwai cikakken hadin kai tsakanin masarautar Kano da bangaren zartarwar gwamnati.
Da yake jawabin godiya mai martaba sarkin Kano ya yi kira ne ga jama'a da su kasance masu hakuri da rikon amana da kyautatuwar zamantakewa a tsakaninsu.
Wakilin mu dake Kano Garba Abdullahi Bagwai ya bamu rahoton cewa an gudanar da bikin cikin tsauraran matakan tsaro.