in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nigeriya sun cafke 'yan tsagera 56 a arewa maso gabashin kasar
2013-06-01 17:02:07 cri
Muhukunta a Shalkwatar tsaro ta kasar Nigeriya dake Abuja a jiya Jumma'a 31 ga watan Mayu, suka tabbatar da cafke wassu karun 'yan tsagera su 56 a arewa maso gabashin kasar.

A cikin wata sanarwar da ta fito daga rundunar tsaron, an ce sojoji ne suka kame wadannan 'yan tsageran a ranar Alhamis bayan da suka samu wani bayani cikin sirri inda aka fallasa maboyar su a wani kauye kuma a boye aka bi sahun wassu daga cikin 'yan tsageran da suke tafiya a wani mota kirar Jeep da suka sata don neman abinci inda nan take aka damke su.

An samu makamai masu dimbin yawa da harsasai lokacin da aka kame wadannan 'yan tsageran wanda a ciki akwai ababen fashewa pakiti 7, bindigogin harba roka guda biyu, abin tada bam, kananan bindigogi da manya.

Lokacin da aka kai masu samamen an lura cewa har sun fara gina wassu sansanin, inji sanarwar.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China