Wannan tasha zata zama tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa mafi girma a Najeriya, wadda za'a yi bikin kafa tubalin gina ta a ranar Talata na mako mai zuwa,kuma shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, Gwamnan jihar Niger Dr. Babangida Aliyu, ministan kula da harkokin wutar lantarki na Najeriya Prof. Chinedu Nebo, karamar ministar samar da wutar lantarki Hajiya Zainab Kuchi da sauran manyan jami'ai za su halarta.
Manyan kamfanonin kasar Sin, wato kamfanin CNEEC, da kamfanin SINOHYDRO ne suka dauki nauyin gina wannan tasha a cikin nan da shekaru biyar masu zuwa.
Haka kuma, za'a yi hayar ma'aikata 'yan Najeriya sama da dubu biyu a wajen wannan aiki, abun da zai warware matsalar rashin guraban ayyukan yi sosai.
Najeriya tana fama da matsalar karancin wutar lantarki, abun da ke jawo cikas ga ci gaban harkokin masana'antun kasar sosai. Bayan da aka kammala aikin, wannan babbar tasha zai taimaka sosai wajen samar da wutar lantarki cikin tsawon lokaci a wurin, da bunkasa tattalin arziki da kuma kyautata zaman rayuwar al'umma a Najeriya.
Wannan tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa dake garin Zungeru na jihar Niger, zata kyautata tsarin samar da wutar lantarki dake wurin, da rage abubuwa masu gurbata muhalli da ake fitarwa, da kuma kiyaye albarkatun man fetur da iskar gas a Najeriya.(Murtala)