in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda na zaman ko ta kwana a kudancin Najeriya dangane da harin kunar bakin wake da aka yi a Kano
2013-03-23 16:10:30 cri
Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Delta mai arzikin mai dake kudancin kasar ta bukaci jami'ai su kasance cikin shiri don hana kai harin ramuwar gayya kan 'yan arewa dake zaune a jihar, sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai tashar manyan motocin daukar fasinja a jihar Kano dake arewa maso yammacin kasar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar Famous Ajie shi ne ya bayyana hakan ga 'yan jarida a garin Asaba babban birnin jihar bayan wata ganawa ta gaggawa.

Ya ce, daukar wannan mataki ya zamo wajibi musamman da yake an san cewa hari irin wannan na iya zuwa garin Asaba daga garin Onitsha na jihar Anambra dake makwabtaka da ita, inda ya kuma kara da cewa, rundunar ta yi tanadin tabbatar da tsaro dangane da harin ramuwar gayya.

A kuma jihar Kano dake arewacin kasar, 'yan sanda sun tabbatar ranar Talata cewa, mutane 22 ne suka rasa rayukansu kana 65 sun jikkata sakamakon fashewar ababai a tashar mota dake unguwar sabon gari, a ranar Litinin da yamma.

An sha fuskantar hare hare a jihar kano, wacce ita ce ta fi yawan jama'a a arewacin Najeriya, kana tana da mabiya addinin Krista da dama.

Zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dau alhakin kai harin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China